Home Labarai Ceto Dalibai: Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya Ta Ba Gwamnati Wa’adi

Ceto Dalibai: Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya Ta Ba Gwamnati Wa’adi

44
0
NANS
NANS

NANS ta ba gwamnati wa’adin mako biyu ta ceto wasu ɗaliban koyan aikin likita 20 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Benue.

Ɗaliban da suka ƙunshi ƴan jihar Borno, da jihar Filato, na kan hanyar su ne ta zuwa jihar Ogun domin halartar wani taro.

Muhammad Sabo, wanda shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar ɗaliban Najeriyar, ya shaida cewa an yi irin wannan abu ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba,

shi ya sa a wannan karo ba za su bayar da ƙofa yadda za a cutar da ɗaliban ba.

Ya bayyana cewa shi ya sa ƙungiyar ta ɗeba wa gwamnati wa’adi domin ganin ta yi duk abin da ya kamata domin kuɓutar da ɗaliban,

ya ƙara da cewa saɓanin hakan zai sa a ga fushin su fiye da yadda aka saba gani.

Ya kuma nuna takaici kan yadda makarantun Najeriya da dama ke fama da matsalar tsaro, wanda hakan ya sanya aka rufe wasu makarantun da dama.

Leave a Reply