Home Home CBN Ya Kashe Naira Biliyan 125.3 Kan Tsaron Nijeriya

CBN Ya Kashe Naira Biliyan 125.3 Kan Tsaron Nijeriya

1
0

Babban Bankin Nijeriya CBN, ya ce ya kashe Naira biliyan 125 da miliyan 300 a kan sha’anin tsaron Nijeriya a shekarar da ta gabata, adadin da ya kusan ninkawa sau uku idan aka kwatanta da kudaden da ya kashe a shekarun baya-bayan nan.

Jaridar Kasuwanci ta Business Day, ta ambato wasu alkaluma da su ka nuna cewa bankin ya kashe Naira biliyan 507 a kan harkokin tsaron kasa, da bangaren soji da kuma sha’anin tsaron jihohi da dai sauran su a tsakanin shekarata 2014 zuwa 2022.

Bankin CBN, ya ce kudaden da aka kashe sun hada da wadanda aka yi amfani da su wajen aiwatar da ayyukan shiga tsakani da su ka shafi sha’anin tsaron kasa na gwamnatin tarraya da na jihohi, da kuma ayyukan inganta fannin kudin Nijeriya idan bukatar hakan ta taso.

Bayanan da jaridar sun tattaro cewa, duk kudaden da aka biya na ayyukan shiga tsakani a madadin gwamnatin tarayya da bankin ya yi, an kashe su ne kamar yadda aka bukace su, sai dai an ware su a matsayin rance sai bayan watanni 12, idan ba a kai ga maida su ga gwamnatin tarayya ba sai su shiga cikin lissafin kudaden da aka kashe.