An tsayar da ranar karawa a Carabao Cup fafatawar zagaye na uku tsakanin Brentford da Arsenal zuwa 27 ga watan Satumba.
Karon farko da za su kara a kofin tun bayan 2018, bayan da Gunners ta ci 3-0 a Emirates.
Sannan Arsenal ta ci 3-0 a gidan Brentford a Satumbar 2022 a Premier League, inda William Saliba da Gabriel Jesus da kuma Fabio Vieira suka ci mata kwallayen.
Ranar 11 ga watan Fabrairu, Arsenal da Brentford suka tashi 1-1 a Emirates, inda Leandro Trossard ya fara cin kwallo Ivan Toney ya farke.
Arsenal, wadda take ta biyar a teburin Premier League ta hada maki 10, yayin da Brentford take ta shida a teburin mai maki takwas.
You must log in to post a comment.