Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Canjin Takardun Kuɗi: Na San Za Ku Sha Wahala – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana jimamin sa da yadda ‘yan Nijeriya ke shan azaba sakamakon sauya fasalin takardun Naira, sai dai ya ce shan azabar ya zama wajibi, matuƙar Nijeriya ta na son ta kawo ƙarshen matsalar annobar cin hanci da rashawa da kuma bunƙasa tattalin arziki.

Buhari ya bayyana haka ne, ta bakin Ministar Kuɗi da Tsare- tsare Zainab Ahmed, bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Ta ce Shugaba Buhari ya yi matuƙar damuwa da halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, amma ta ce hakan ya zama wajibi domin ya na faruwa ne sakamakon canjin da ake ƙoƙarin samarwa.

Ministar ta ƙara da cewa, wannan manufa an daidaici lokacin da ya dace ne wajen aiwatar da ita, don haka ta na da nata alherin na wawure ɗimbin dukiyar da aka sace aka danƙare su wuri guda.

Exit mobile version