Gwamnatin jihar Neja ta bada umurnin kama duk dan kasuwar da yak i amsar tsaffin takardun kudi.
Sakataren gwamnatin Jihar Alh. Ahmed Ibrahim Matane, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a Minna a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa har yanzu tsofaffin takardun Naira na nan daram kuma duk wanda aka kama ya ki karbar su domin yin kasuwanci to zai fuskanci fushin doka.
A cewar sa, tsoffin takardun Naira na nan daram kuma duk wanda aka kama ya ki karba yana jawo wa ‘yan kasa wahala za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.
Ibrahim Matane, ya bukaci al’ummar jihar su gudanar da harkokin su na yau da kullum sannan su kai rahoton duk mutumin da ya ki karbar tsaffin kudin ga jami’an tsaro a jihar domin daukar matakin da ya dace.