Kasar Burtaniya, ta ce ta sa ido a kan ‘yan siyasa da jam’iyyu da jami’an tsaro da duk wanda zai haifar ko haddasa rikici ta shafukan sada zumunta gabannin zaɓen shekara ta 2023 a Nijeriya.
Jakadiyar Burtaniya a Nijeriya Catriona Laing ce ta sanar da haka, yayin ganawa da kwamitin gudanarwa na harkokin zaɓe na jam’iyyar PDP a Abuja.
Ta ce zaɓen shekara ta 2023 ya na da muhimmanci ga Afirka da ma duniya baki ɗaya, don haka dole ido ya na kan Nijeriya kuma Burtaniya za ta sa ido a kan ta.
Catriona Laing, ta ce Burtaniya ta damu matuƙa a kan abubuwan da su ka faru na baya-bayanan, ciki kuwa har da rikice-rikice 52 da ke da alaƙa da zaɓe a jihohi 22, da kuma harin da aka kai wa tawagar yakin neman zaben PDP a jihar Borno.
Ta ce Burtaniya ba za ta goyi-bayan kowace jam’iyya ba, domin ta na da burin ganin kowane ɗan kasa ya samu damar zaɓen abin da ya ke ganin shi ne cancanta a gare shi.