Home Home Burkina Faso: Gwamnati Ta Musanta Yunkurin Juyin Mulki

Burkina Faso: Gwamnati Ta Musanta Yunkurin Juyin Mulki

200
0

Gwamnatin Burkina Faso ta tabbatar da harbe-harben da aka rika yi a babban birnin kasar na Ouagadougou.

Kamfanin dillancin labarai na AFP cikin wani sakon Twitter ya ce an rika jin karar harbe-harben daga barikin sojoji ciki har da wasu biyu da ke Ouagadougou, wata majiya ta shaida wa kamfanin cewa an ji harbe-haben a garin Kaya da ke aewacin kasar bayan wanda aka ji a babban birnin.

Kakakin gwamnatin Alkassoum Maiga ya ce “labarin juyin mulkin ba gaskiya ba ne, kuma gwamnati na kira ga mutane su kwantar da hankalinsu.”

Kzalika ta kara musanta cewa an tsare shugaban kasar a wani abu mai kama da juyin mulki.

Ministan tsaro na kasar ya ce tuni aka shawo kan wannan rikici, duk da cewa har yanzu ana jin karar wasu ana jin karar harbi a wasu bariki da ke kusa.

A ranar 11 ga watan Janairu, rahotannin sun ce sai da aka kama sojoji 10 kan zargin kitsa juyin mulki.

Dama dai gwamnatin kasar na fuskantar zanga-zangar kan gazawarta na kawo karshen hare-haren da ake masu ikirarin jihadi da suka munanan ayyukansu a Afrika Ta Yamma tun 2015.

Leave a Reply