Home Labaru Kasuwanci Bunkasa Kasuwanci: Shugaba Buhari Ya Halarci Wani Taro A Kasar Nijar

Bunkasa Kasuwanci: Shugaba Buhari Ya Halarci Wani Taro A Kasar Nijar

314
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tafi Jamhuriyar Nijar inda za a bude wani  taron shugabannin kasashen Afirka karo na 12.

Fadar shugaban ta bayyana haka a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Tuwita, inda ta ce  shugaba Buhari zai halarci taron kungiyar shugabannin kasashen afrika wanda zai mai da hankali akan maganar kasuwancin Nahiyar Afirka gaba daya.

Ta ce taron za a  kaddamar da sabon tsarin kasuwanci domin kasashen Afirka wanda aka yi wa suna kasuwanci mara shinge, wanda ya kunshi  bude shafin yanar gizo na musamman domin kula da tsarin da hanyar biyan kudi ta zamani da kuma bangaren lura da abinda ke gudana.

Gabanin halartar taron shugaban kasa Buhari ya tuntubi masana da kuma kwararru a Najeriya kan harkar kasuwanci sannan daga baya ya amince da cewa Najeriya za ta kasance cikin yarjejeniyar.