Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Bunkasa Kasuwanci: Gwamnatin Kano Za Ta Hada Hannu Da Kasar Dubai

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci babban Ofishin Jakadancin hadaddiyar daular Larabawa da ke Abuje, domin samar da alaka a tsakanin jihar Kano da mahukunta ofishin.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Ya ce idan wannan tattaunawa ta samu nasarar da ake fata, za a fara  yin ayyukan ci gaba na duniya irin na zamani, tsakanin jihar Kano da kuma kasar Dubai,  wanda aka yi wa lakabi da samar da tagwayen birane wato Twin City Concept, da nufin samar da alakar kasuwanci ta kusa da kusa.

Wannan na kunshe ne cikin jawabin da Jakadan Kasar Dubai, Fahad  Obaid Al-Taflak, ya gabatar a lokacin da gwamna Ganduje, ya ziyarce shi a Ofishin Jakadanci Kasar da ke Abuja.

Ya ce ya na ba gwamnan tabbacin kulla alaka ta tagwayen biranen,  a tsakanin jihar Kano da kasar Dubai domin ci-gaba baki daya.

Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira tare da bukatar jiragen sama na kasar ta Dubai, su rika zuwa suna sauka a babbar tashar jiragen sama ta Malam Aminu Kano da ke Jihar Kano, duba da yadda tashar ke gamsar da fasinjojin duniya.

Exit mobile version