Home Labaru Ilimi Bunkasa Ilimi: Nakasassu Za Su Fara Karatu Kyauta A Kano – Ganduje

Bunkasa Ilimi: Nakasassu Za Su Fara Karatu Kyauta A Kano – Ganduje

506
0
Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya shelanta bayar da ilimi kyauta ga Nakasassu dake Jihar.

Ganduje, ya bayyana hakan na a lokacin da ake  bikin karban mulkin Jihar, inda  yi alkawarin bayar da ilimi kyauta ga dukkanin yaran Jihar da suka isa shiga makaranta.

Ya ce  gwamnatin jihar  Kano za ta yi rangwame ga ‘yan asalin Jihar da suke cikin manyan makarantun Jihar, ya kara da cewa, gwamnati za ta yi amfani da nasarorin da ta samu a zangonta na farko a sassan ilimi da noma da manyan ayyuka da kuma sashen kula da Lafiya.

Ya ce, zangon mulkin na biyu zai samar da wata sabuwar hukuma mai suna, Kano State Small Town Water Supply Agency, wacce za ta kula da samar da ruwa ga al’ummomin da ke a karkara.

Ganduje, ya sabunta aniyarsa ta yakar cin hanci da rashawa, ya kara da cewa, zangon mulkin sa na biyu zai tabbatar da farfado da hukumar hana cin hanci da karbar rashawa ta Jihar ta yadda za ta yi aikin ta tukuru.

Abdullahi Umar Ganduje, ya yi alkawarin gudanar da gwamnatin da za ta kunshi kowa da kowa ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba, ya yi nuni da cewa, zamanin siyasa kuma ya wuce.

Leave a Reply