Gwamnatin tarayya ta amince da biyan naira dubu 75 a matsayin alawus-alawus na kowane zangon karatu wato Semester ga daliban da ke karatun digiri a fannin Ilimi a jami’o’in gwamnati.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya sanar da hakan a bikin ranar malamai ta duniya da aka gudanar a Abuja.
Adamu, wanda babban sakataren ma’aikatar Ilimi ta tarayya, Sonny Echono, ya karanta jawabinsa a taron, ya ce ma’aikatar sa za ta hada kai da gwamnatocin jihohi domin tabbatar da samar da aikin yi ga daliban kai tsaye kan kammala karatun.
Daliban ke karatun NCE za su karbi naira dubu 50 a matsayin alawus na kowane zangon karatu wato Semester a wani kokarin gwamnati domin jawo hankalin samar da kwararrun malaman makaranta.