Home Labaru Ilimi Bunkasa Ilimi: Gwamna Zullum Ya Saka Marayu Fiye Da 5,000 Makaranta A...

Bunkasa Ilimi: Gwamna Zullum Ya Saka Marayu Fiye Da 5,000 Makaranta A Monguno

84
0
Zulum Ya Mika Tallafi Ga Gidaje 10,000, A Garin Ran Da Ke Higar Borno
Zulum Ya Mika Tallafi Ga Gidaje 10,000, A Garin Ran Da Ke Higar Borno

Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya saka marayu fiye da dubu biyar wadanda iyayensu suka mutu a rikicin Boko Haram a makaranta.

Gwamna Zulum wanda shi da kansa ya kai yaran makaranta a Monguno ya kuma jagoranci daukan bayanansu ya shafe kwanaki biyu yana tantace daliban 5,361.

Sanarwar da kakakin gwamnatin Isa Gusau ya fitar, ta ce yaran da shekarunsu ke tsakanin 7 zuwa 13, kowanne su za abasu kayan makaranta da littafan karatu da abinci.

Gwamnan ya kuma sanar da cewa zai dau malaman Ismaliyya domin su rinƙa koyar da su Ilimin Addini.

Sanarwar ta kuma ce gwamnan ya amince da bai wa yaran rundunar tsaro ta Civilian JTF, da mafarauta da ke yaki da Boko Haram tallafin karatu daga matakin firamare har zuwa makarantun gaba da sakandare.