Home Labaru Ilimi Bunkasa Ci Gaba: Gwamnatin Kadunata Ɗaura Ɗamarar Amfani Da Fasahar Zamani Domin...

Bunkasa Ci Gaba: Gwamnatin Kadunata Ɗaura Ɗamarar Amfani Da Fasahar Zamani Domin Inganta Harkokin Mulki

73
0

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ce gwamnatin sa ta himmatu wajen yin amfani da karfin fasahar zamani wajen bunkasa tattalin arziki, da inganta harkokin mulki da inganta rayuwar al’ummar jihar baki daya.

Gwamna Uba Sani, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya ke kaddamar da bude taron koli na baje kolin fasahar zamani ta mutum-mutumi wato (AI Robotics) karo na uku wanda kungiyar masana Kwamfuta ta Nijeriya, NCS ta shirya gudanarwa a Kaduna, ya ce batun ci gaban fasahar mutum-mutumi, gwamnatin Kaduna ba za ta bari a bar ‘yan jihar ta a baya ba.

Gwamnan, wanda mataimakiyar sa, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta wakilta ya bayyana cewa, al’ummomin da suka yi watsi da fasahar kere-kere ta zamani, za a bar su a baya saboda (AI Robotics) sun zama wani jirgin ruwan tsira da dole sai an shiga in ana neman tsira.

Dakta Hadiza Balarabe Sabuwa, ta kuma yabawa NCS bisa lambar yabo da ta Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani a matsayin Gwarzon Gwamna kan fasahar zamani ta Nijeriya ta 2023 da aka gudanar a jihar Legas.

Shima da yake nasa jawabin, shugaban NCS  na kasa, Dr. Muhammad Sirajo Aliyu, ya godewa gwamna Uba Sani na jihar Kaduna da ya karbi bakuncin taron, da kuma tallafin da gwamnan ya ba kungiyar.

Leave a Reply