Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun juma’a, 19 ga wata da kuma ranar Litinin 22 ga wata a matsayin rakunan hutu domin gudanar da bukukuwan Easter a sassa daban-daban na Najeriya.
Ministan harkokin cikin gida Laftanar Janar Abdurrahman Danbazau, wanda ya sami wakilcin Sakatariya a ma’aikatar Georgina Ehuriah, ya bayyana haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.
Ministan ya bukaci mabiya addinin Kirista a Najeriya su yi koyi da kyawawan dabi’u na soyayya da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma a bukukuwan Easter.
Janar Dambazau, ya yi kira ga ‘yan Najeriya na gida da kuma na waje, su yi amfani da wannan lokaci wajen gudanar da addu’o’i na zaman lafiya da kuma hadin kai domin ci gaban Najeriya.
Daga karshe ministan na harkokin cikin gida Janar Abdurrahman Danbazau, ya bukaci al’ummar Najeriya su cigaba da goyon bayan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a dai dai lokacin da ta sa ayyukan ci gaba, a gaban ta.