Home Labaru Bukatar Shiri: Majalisar Dattawa Ta Dage Zaman Ta Zuwa Ranar 2 Ga...

Bukatar Shiri: Majalisar Dattawa Ta Dage Zaman Ta Zuwa Ranar 2 Ga Watan Yuli

309
0

Majalisar dattawa ta dage zaman ta zuwa ranar Talata, 2 ga watan Yuli domin bada damar yin rabe-raben kujeru da ofisoshi ga sanatoci.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ovie Omo-Agege ya gabatar da bukatar hakan, yayin da Sanata Philip Aduda ya mara masa baya, bayan an share tsawon sa’a daya ana ganawa.

Yanzu haka dai majalisar ta kafa kwamitin wucin-gadi na mutane 12 a karkashin jagorancin Sanata Abu Kyari, wanda aka dora wa alhakkin hada kai da hukumar gudanarwa ta  majalisar domin jin dadin Sanatoci.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya ce an ba kwamitin tsawon makonni biyu ya gabatar da rahoton sa, kuma zai zai yi aiki ne tare da magatakardar majalisar Nelson Ayewoh.