Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da yi wa shugaban hukumar kula da gidajen yari na Najeriya, Ja’afaru Ahmad, karin wa’adi na shekara guda da zai fara daga ranar 21 ga watan Yulin nan.
Sanarwar da ta fito daga mai magana da yawun hukumar kula da harkokin cikin gida, Muhammad Manga.
Manga, ya ce an yi wa Muhammad Ja’afar karin wa’adi na shekara guda ne saboda irin ayyukan cigaba da ya faro a hukumar.
Ya cigaba da cewa
ayyukan sun hada da kula da hakkin dan adam, da inganta kiwon lafiya, da
samar da ilimin ayyukan noma ga
fursunoni da suka cancanci ya kara sa su.