Home Labaru Buhari Ya Yi Wa Saraki Bi-Ta-Da-Kulli – Inji Atiku

Buhari Ya Yi Wa Saraki Bi-Ta-Da-Kulli – Inji Atiku

442
0
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa , Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar, PDP
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa , Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar, PDP

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin shugaba Buhari da yi wa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki bi-ta-da-kulli.

Atiku ya bayyana haka ne, yayin da ya ke tsokaci game da binciken da Hukumar EFFC ke gudanarwa a kan Bukola Saraki, ya na mai cewa tun a baya an gudanar da bincike a kan batutuwan da EFFC ke gudanar da bincike a kai a halin yanzu.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku Abubakar ya ce duk da cewa ya na goyon bayan binciken masu aikata rashawa, ya na ganin ba daidai ba ne yin amfani da gwamnati wajen yi wa ‘yan adawa bi-ta-da-kulli.

Ya ce Saraki ya na daya daga cikin ‘yan siyasar da aka tsananta bincike a kan su a Nijeriya, bayan an gudanar da bincike a kan sa har zuwa Kotun Koli, kuma ya yi nasara a kan wadanda ke zargin sa.

Leave a Reply