Home Home Buhari Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan ‘Yan Najeriya A Burkina Faso

Buhari Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan ‘Yan Najeriya A Burkina Faso

29
0
Buhari Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan 'Yan Najeriya A Burkina Faso

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi Allah-wadai da kisan ‘yan Nijeriya, waɗanda ke kan hanyar su ta zuwa ziyarar ibada garin Kaulaha na ƙasar Senegal.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa Garba Shehu ya fitar, ya ce Buhari ya samu mummunan labarin harin da aka kai wa ‘yan Nijeriya a kan haryar su ta zuwa Kaulaha na ƙasar Senegal.

Wasu ‘yan bindiga ne su ka afka wa ayarin motocin da ke ɗauke da mutanen a ƙasar Burkina Faso, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe wasu da dama.

Shugaba Buhari, ya jajenta wa iyalan waɗanda su ka mutu, tare da addu’ar samun kariya ga waɗanda su ka maƙale a can.