Home Labaru Buhari Ya Tsawaita Zamansa A Landan Domin Duba Lafiyar Haƙorinsa

Buhari Ya Tsawaita Zamansa A Landan Domin Duba Lafiyar Haƙorinsa

378
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tsawaita zaman sa a
London da tsawon mako guda domin duba lafiyar haƙoran sa,
kamar yadda mai magana da yawun sa Femi Adesina ya
bayyana.

Idan dai baa manta ba, shugaba Buhari ya je London ne domin halartar bikin naɗin sarkin Ingila charles lll.

Tun da farko an tsara cewa, shugaba Buhari zai dawo Nijeriya a cikin wannan makon, amma yanzu zai ƙara mako guda domin ganawa da likitan haƙoran sa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, mai Magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina, ya ce Likitan Buhari ya buƙaci ya ƙara ganin sa ne nan da kwanaki biyar domin ci-gaba da lura da yanayin haƙoran sa.

Leave a Reply