Home Labarai Buhari Ya Nemi ’Yan Takara Su Yi Kamfe Babu Cin Mutunci

Buhari Ya Nemi ’Yan Takara Su Yi Kamfe Babu Cin Mutunci

55
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shaida wa ‘yan takara zaben shekara ta 2023 dama ce ta bauta wa Nijeriya, sannan ya ya bukaci ‘yan takara su guji keta rigar mutunci da tunzura jama’a a yakin neman zaben su.

Shugaba Buhari ya yi gargadin cewa, karuwar labarun karya da na ci-gaba da zama gagarumar barazana ga tsarin dimokradiyyar Nijeriya.

Ya ce labarun karya su na dauke hankali daga gudanar da yakin neman zabe bisa manufa, maimakon haka sai a yi ta kwarzanta yiwuwar cin mutuncin mutane da zaga-zage tare da harzuka mutane.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne, a wani sakon bidiyo da ya gabatar wajen taron sa hannun ‘yan takarar shugaban kasa domin tabbatar da zaman lafiya a zaben shekara ta 2023.