Home Labaru Buhari Ya Kira Ministan Lantarki Kan Matsalar Wuta Da Ake Fama Da...

Buhari Ya Kira Ministan Lantarki Kan Matsalar Wuta Da Ake Fama Da Ita

79
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kira Ministan Lantarki Abubakar Aliyu domin ganawa a sirrance a fadar shi da ke
Abuja.

Ana sa ran shugaba Buhari zai tattauna da Ministan ne kan
matsalar wutar lantarki da ake fama da ita a fadin Nijeriya.

Wannan, ya na dauke ne a cikin wata sanarwa da mai magana da
yawun shugaban kasaGarba Shehu ya fitar.

Shugaba Buhari, ya kuma kira Gwamna Hope Uzodinma na
jihar Imo da mai ba shi shawara a kan tattalin arziki Doyin
Salami domin ganawa da su.