Home Labaru Buhari Ya Karyata Tura Sunayen Ministoci

Buhari Ya Karyata Tura Sunayen Ministoci

537
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Fadar Shugaban kasa, ta karyata jerin sunayen ministocin da ke yawo a shafukan sada zumunta na zamani.

Da ya ke maida martani a kan sunayen, mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu, ya bukaci jama’a su yi watsi da rahoton da aka alakanta da shi.

Ya ce duk wanda ya ke son sanin abin da ya fadi ya je shafin sa ba na bogi ba, domin ba ya da wani sabon labari a kan nadin ministoci.

Garba Shehu ya cigaba da cewa, ya na bukatar mutane su yi watsi da rahoton da aka alakanta da shi, domin bay a da tushe balle makama.