Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin farfado da kamfanin karafan na Ajaokuta da ya durkushe kusan shekaru 40 a jihar Kogi.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin farfado da kamfanin ne a ranar Litinin din da ta gabata, domin ganin an fadada tattalin arzikin Nijeriya.
Kwamitin mai mutane 13, an yi masa lakabi da Ajaokuta Presidential Project Implementation Team, kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne zai jagoranci shi.
Boss Mustapha ya kara da cewa, gwamnatin tarayya na sha’awar farfado da kamfanin ne domin ganin tattalin arzikin Nijerita ya dai-dai-ta.
Kamfanin Ajaokuta dai, ya kasance a wani yanai ya rai kwakwai mutu kwakwai har na kusan tsawon shekaru 40 ba tabuka komai, sannan an yi yunkurin farfado da kamfanin a baya amma lamarin ya ci tura, wanda hakan ya zanyowa Nijeriya asarar makudan kudade.
Shugaban kwamitin Boss Mustapha ya ce, za a yi aiki ne karkashin wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da bankin Afrexim da wani kamfanin kasar Rasha bisa wasu sharudda da aka kafa.