
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da aikin haƙar rijiyar man fetur a ƙaramar hukumar Obi ta jihar Nasarawa.
Ƙaddamar da aikin tona rijiyar dai, zai sa kamfanin mai na ƙasa NNPC ya fara tono man fetur daga jihar.
A cikin watan Nuwamba na shekarar da ta gabata ne, shugaba Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙo man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.
Yawancin man da Nijeriya ke da shi dai ta na haƙo shi ne daga yankin Niger Delta a yankin kudu maso kudu.
You must log in to post a comment.