Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana irin mutanen da ya ke muradin nadawa a mukamin ministoci a sabuwar gwamnatin sa, inda ya ce kwararru kuma amintattu kawai zai yi aiki da su.
Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi bakuncin shugabannin majalisar dokoki a wata liyafar cin abinci da ya shirya masu a fadar sa da ke Abuja.
Shugaba Buhari, ya ce ya na fuskantar matsin lamba daga bangarori daban-daban a kan nadin sabbin ministocin, amma ya ce duk da matsin lambar, mutanen da ke da inganci, kwararru kuma amintattu kawai zai nada.
Ya ce ya san mutane da dama sun kosa su ga sunayen ministocin da zai nada don hankalin su ya kwanta, sai dai ya ce daga cikin tsofaffin ministocin sa bai san da yawa daga cikin su ba.
Buhari ya cigaba da cewa, ya dai karbe su ne daga jam’iyyar su da wasu mutanen sa, amma a yanzu zai bi a hankali ya zabo wadanda ya sani da kan sa.