Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Budurwa Ta Maka Mahaifinta A Kotu Kan Auren Dole A Kaduna

Wata budurwa mai shekaru 20, ta maka mahaifin ta kotu bisa
kokarin yi mata auren dole a Kaduna.

Matashiyar mai suna Fatima Aliyu ta shaida wa kotun shari’ar Musulunci cewa ta na da wanda take so, amma mahaifin ta ya na kokarin yi mata auren dole.

Mahaifin yarinyar dai ya shaida wa kotun cewa kafin iyayen sa su rasu ne su ka zaɓa wa yarinyar mijin aure, shi ya sa ya ke kokarin cika alkawari.

Mai shari’a Malam Aiyeku Abdulrahman, ya ce duk da ya k mahaifi ya na da damar zaɓa wa ‘yar sa mijin aure, amma a wannan gabar kokarin tilasta mata bai dace ba, don haka ya shawarci mahaifin ya kara hakuri da diyar sa.

Alkalin, ya bukaci mahaifin ya ba yarinyar damar gabatar da mutumin da ta ke so sannan a yi bincike, idan babu wani laifi a bar su su yi auren su.

Exit mobile version