Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Bude Makarantu: Kungiyar ASUU Ta Yabawa Matakin Gwamnatin Tarayya

Kungiyar malamai ta ASUU ta goyi bayan shawarar da gwamnatin tarayya ta yanke na dakatar da daliban aji shida daga za na jarrabawar WAEC da aka shirya farawa a ranar 4 ga watan Agusta.

Kungiyar ta shawarci gwamnatin tarayya da ta bar makarantu a rufe har zuwa shekarar 2021 domin tabbatar da ingantaccen shiri kafin a sake buɗe su.

Kungiyar ASUU ta buga misali da hukuncin da gwamnatin kasar Kenya ta yanke na cewa kafatanin makarantu a kasar za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai shekara mai zuwa.

A wata hira da shugaban ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya yi da manema labarai ya ce kar a kuskura a yi sakaci da lafiyar dalibai.

Farfesa Ogunyemi,  ya ce kada a sake a buɗe makarantu har sai gwamnatin tarayya ta samu yarjewa ta iyayen yara kuma sun nuna amincewarsu a kan hakan.

Exit mobile version