Home Labarai Bude Iyakoki: NIS Ta Dage Takunkumin Shige Da Fice A Nijeriya Da...

Bude Iyakoki: NIS Ta Dage Takunkumin Shige Da Fice A Nijeriya Da Nijar

119
0

Sakamakon umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar na sake buɗe kan iyakokin Nijeriya da Nijar, Shugabar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa,  CGI Kemi Nanna Nandap ta Umarci dukkan kwanturololin jihohi da na kula da iyakoki da ke gefen iyakokin Nijeriya da Nijar su tabbatar da aiwatar da umurnin.

Shugabar hukumar ta umarci kwanturololin su ɗage takunkumin shige da ficen mutane da kayayyaki a kan iyakokin.

Hukumar ta NIS ta tabbatar wa al’umma cewa a shirye take wajen kula da shige da fice a kan iyakokin Ƙasa bisa ƙa’ida tare da kiyaye mutunci da tsaron iyakokin Nijeriya.

Babban Shugaban Shiyya ta Uku (Zone C), da ta kunshi jihar Adamawa, da Bauchi, da Borno, da Gombe, da Yobe da Filato, mataimakin Kwanturola Janar (ACG) James Sunday, ya kai ziyarar aiki a jihohin Borno da Yobe da ke Arewa maso Gabas domin lura da yadda ake bude kan iyakar.

Leave a Reply