Home Labaru Brazil Ta Samu Tikitin Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya Ta 2022

Brazil Ta Samu Tikitin Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya Ta 2022

104
0

Brazil ta samu gurbi a gasar cin kofin Duniya ta 2022 da za ta gudana a Qatar inda ta zama kasa ta 4 da zuwa yanzu ta samu wannan gurbi kuma ta farko daga kudancin Amurka.

Kasashen da zuwa yanzu ke da tikitin shiga gasar sun kunshi Qatar mai masaukin baki da Jamus mai tarihin daga kofin sau 4, kana Denmark tukuna ita Brazil din bayan wasanta na yau da ta yi nasara kan Colombia da kwallo 1 mai ban haushi.

Brazil na matsayin mafi tarihin daga kofunan gasar ta cin kofin Duniya bayan dagawa har sau 5 tsakanin shekarun 1958 da 1962 da kuma 1970 baya ga shekarar 1994 da 2002.

Haka zalika kasar ta Brazil na jerin kasashen da basu taba fashin samun tikiti a gasar ta cin kofin Duniya ba tun bayan farota a shekarar 1930.

Gasar ta cin kofin Duniya bisa al’ada na kunsar tawagar kasashe 32 tun bayan fadadata a shekarar 1998, a wannan karon za ta faro ne daga ranar litinin 21 ga watan Nuwamban 2022 zuwa ranar lahadi 18 ga watan Disamban shekarar inda kasashe 31 kan fafatawa don gurbin yayinda mai masauki baki ke samun gurbi a bagas.