Home Labaru ‘Yan Sanda A Afrika Ta Kudu Sun Tarwatsa ‘Yan Biafra Da Su...

‘Yan Sanda A Afrika Ta Kudu Sun Tarwatsa ‘Yan Biafra Da Su Ka Yi Wa Buhari Ihu

778
0
‘Yan Sanda A Afrika Ta Kudu Sun Tarwatsa ‘Yan Biafra Da Su Ka Yi Wa Buhari Ihu
‘Yan Sanda A Afrika Ta Kudu Sun Tarwatsa ‘Yan Biafra Da Su Ka Yi Wa Buhari Ihu

Jami’an yan sanda a kasar Afrika ta Kudu sun yi harbi a kan mai uwa da wabi domin tarwatsa wani gungu ‘yan kungiyar Biafra da suka yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ihu a lokacin da ya kai ziyara kasar.

‘Yan kungiyar dai, sun yi alkawarin za su ci zarafin shugaba Buhari idan har ya je kasar ta Afrika ta Kudu.

Sai dai jami’an ‘yan sandan kasar da ke Pretoria sun tarwatsa ‘yan kungiyar ta Biafra, inda suka rika harbi wanda hakan ya yi sanadiyar raunar da wasu daga cikin su.

Wannan mataki da hukumar ‘yan sandan kasar ta dauka dai, ya kawo karshen ihun da ‘yan kungiyar Biafra su ka yi wa shugaban kasa Buhari.

Idan dai ba a manta ba, shugaban kasa Buhari ya je kasar ta Afrika ta Kudu ne a ranar Larabar da ta gabata domin samun masalaha akan lamarin da aka kai wa ‘yan Nijeriya a wasu makonnin da suka gabata a kasar ta Afrika ta Kudu.