Home Labarai Bola Tinubu Ya Yi Amai Ya Lashe Kan Karewar Wa’Adin Katin Zabe

Bola Tinubu Ya Yi Amai Ya Lashe Kan Karewar Wa’Adin Katin Zabe

142
0

Jagoran jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya yi amai ya
lashe, dangane da maganar da ya yi cewa wa’adin amfani da katin zabe ya kare.

A wata sanarwa da ofishin yada labarain sa ya fitar, ya ce
Tinubu ya yi kuskuren ambaton kalmar karewa a harshen
Turanci ne, maimakon ya ce watakila akwai bukatar a sabunta
katin.’

Sanarwar dai ta biyo bayan ce-ce-ku-cen da kalaman Tinubu su
ka janyo, lamarin da ya sa hukumar zabe ta kasa ta yi ma shi
martani da cewa wa’adin amfani da katin bai ƙare ba, don haka
za a cigaba da amfani da shi wajen kaɗa ƙuri’a.

A wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta, an ga Bola
Tinubu sanye da takunkumi a fuskar sa kuma zagaye da mutane,
inda ya ke cewa wataƙila ba za su gaya maku a kan lokaci ba,
amma wa’adin amfani da katunan zaɓe ya ƙare, don haka akwai
buƙatar yaɗa hakan a ƙananan hukumomi da mazaɓu.

Leave a Reply