Home Labaru Boko Haram: Rashin Murabus Ɗin Manyan Hafsoshi Ya Tsawaita Yaƙi Da ‘Yan...

Boko Haram: Rashin Murabus Ɗin Manyan Hafsoshi Ya Tsawaita Yaƙi Da ‘Yan Ta-Da-Ƙayar-Baya – Monguno

362
0

Mai tsawatarwa na majalisar wakilai ya ɗora alhakin gazawar dakarun sojin ƙasa na kawo ƙarshen yaƙi da Boko Haram kan rashin karsashin aiki saboda komai girman matsayin hafsa, ba zai kai maƙura a muƙamin soja ba.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mohammad Tahir Monguno

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mohammad Tahir Monguno, ya ce matsalar ta janyo dakushewar tsimi da rashin kuzarin sojoji, waɗanda kuma ke shafar yaƙin da Najeriya ke yi da Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Monguno na wannan jawabi ne yayin binciken da majalisar wakilai ke yi bayan sanar da murabus ɗin wasu sojoji 365 farat ɗaya.

A cewar sa, riƙe wasu hafsoshi da gwamnatin ƙasar ta yi na sanya manya-manyan sojoji a Najeriya kai wa shekarun barin aiki ba tare da sun samu damar da suka cancanci samu ba.

Rikicin na Boko Haram dai ya shafe tsawon shekara 11, kuma har yanzu ƙungiyoyin ‘yan ta-da-ƙayar-bayan da suka rabu zuwa ISWAP da Boko Haram na ci gaba da kai ƙazaman hare-hare a yankin Tafkin Chadi.