Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Boko Haram: Malamai 2,295 Suke A Jihohin Borno, Yobe Da Adamawa Inji Ministan Ilimi

Ministan kula da harkokin Ilimi Adamu Adamu ya ce a cikin shekaru tara da suka gabata kimanin malaman makaranta 2,295 suka rasa rayukan su yayin da 19,000 suka rasa muhallan su sakamakon rikicin Boko Haram a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Adamu ya kara da cewa, kimanin makarantu 1,500 ne kungiyar Boko Haram ta lalata daga shekara ta 2014 zuwa yanzu, wanda ya ce hakan ya taimaka wajen kara yawan yara da ba su zuwa makaranta a Nijeriya.

Ministan ya ce, tun lokacin da matsalar tsaro ya fara a yankin Arewa maso gabas, bangaren ilimi ya fara fuskantar kalubale saboda yadda ‘yan ta’adda da ke kashe dalibai da malamai, da kuma lalata makarantu.

A karshe ministan ya ce ma’aikatar ilimi tare da hadin gwiwar kungiyoyin UNESCO da UNICEF da cibiyoyin bincike da lissafi na yankunan Nijeriya shida, sun kirkiro wani kudiri na kare yara dalibai da rikice-rikicen matsalar rashin tsaro.

Exit mobile version