Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Boko Haram: Magu Ya Nemi A Rika Lura Da Masu Yawo Da Tsabar Kudi

Ibrahim Magu, Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa, EFCC

Ibrahim Magu, Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa, EFCC

Mukaddashin Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC Ibrahim Magu, ya yi kira ga Sojoji su takaita yawo da kudi a yankin Arewa maso Gabas da ke fama da ta’addancin Boko Haram.

Ibrahim Magu, ya kuma nemi shugaban Dakarun sojin Operation Lafiya Dole Manjo Janar Olusegun Adeniyi, ya tabbatar ana duba kungiyoyi masu zaman kan su wajen zirga-zirga da tsabar kudi.

Magu ya ce ya kamata a rika sa ido, har sai hukuma ta bada dama kafin wata kungiya ta rika kai-komo da dukiya a yankin.

Ya ce hakan zai taimaka wajen dakile ta’adin da ‘yan ta’adda ke yi da makudan kudade.

Ibrahim Magu, ya ce EFCC ta dade ta na sa ido a kan wadanda ke aiki a matsayin masu bada taimako da agajin gaugawa a yankin.

Tuni dai EFCC ta tattara sunayen kungiyoyin da ke aiki a jihohin Borno da Yobe, kuma ana lura da masu yawo da kudin da yawan su ya haura naira miliyan daya don ganin bayan Miyagun da ke fakewa da sunan kungiyoyin.

Exit mobile version