Home Labaru Boko Haram: Gwamna Zulum Ya Kawo ‘Yan Sintiri 150 Daga Kasar Kamaru

Boko Haram: Gwamna Zulum Ya Kawo ‘Yan Sintiri 150 Daga Kasar Kamaru

505
0
Boko Haram: Gwamna Zulum Ya Kawo ‘Yan Sintiri 150 Daga Kasar Kamaru
Boko Haram - Gwamna Zulum

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara, ya shigo da ‘yan sintiri 150 daga kasar Kamaru domin tattara ragowar ‘yan ta’addan Boko Haram daga jihar.

Sabbin ‘yan sintirin daga Kamaru dai za su hada kai ne da mafarautan Nijeriya, da kuma ‘yan sintirin da ke taiamaka wa rundunar sojin Nijeriya, wajen yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram.

 Tuni an mika masu motocin aiki hudu da sauran kayan fada, a wajen wani kwarya-kwaryan biki da aka shirya masu a Damasak, helkwatar karamar hukumar Mobbar da ke yankin tafkin Chadi.

Taron ya samu halartar kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya na jihar Sugun Mai-Mele, da dan majalisar jihar mai wakiltar mazabar Mobbar Usman Moruma da sauran jami’an gwamnatin karamar hukumar.

Gwamnan, ya bayyana shirin sa na yakar ta’addanci a jihar, ta yadda ya dauki dubban mafarauta da ‘yan sintiri daga yankuna daban-daban a arewacin Nijeriya.

Leave a Reply