Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Bitar Zabukan 2019: INEC Ta Ce Zata Inganta Ayykan Ta A Zabukan Da Ke Tafe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta Kasa, INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fara gudanar da bita a kan zabukan shekara ta 2019 domin sake inganta shirin ta a wasu zabukan da ke tafe.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya kara da cewa, hukumar INEC ta fara zaman bitar zaben 2019 a ranar Talatar da ta gabata a Abuja.

Farfesa Yakubu ya ce, ganawar da su ka yi a ranar Talata ita ce ta farko tun bayan kammala zabe, kana kuma ta farko bayan zama da su ka yi domin samun matsaya a kan yadda za’a gudanar da zaben 2019.

Yakubu ya kara da cewa, ya na fatan duk abubuwan da aka tattauna a wajen bitar za su yi wa hukumar amfani domin sake inganta yanayin gudanar da zabuka a Nijeriya.

Bugu da kari, hukumar za ta yi wawaye ta hanyar binciko korafe-korafe da suka shafi irin wannan zaman na shekaru 40 da suka gabata.

Exit mobile version