Home Home Bita-Dakulli: Baitul-Malin Amurka Ya Mika Bayanin Harajin Da Trump Ke Biya Ga...

Bita-Dakulli: Baitul-Malin Amurka Ya Mika Bayanin Harajin Da Trump Ke Biya Ga Majalisa

36
0

Baitul-malin Amurka ya mika wa wani kwamitin majalisar dokokin kasar takardun da ke kunshe da bayanan harajin da tsohon shugaban kasar Donald Trump ke biya.


Hakan ya biyo bayan hukuncin da Kotun Kolin kasar ta yanke ne a makon da ya gabata, inda ta bayar da umarnin bai wa kwamitin da ‘yan jam’iyyar Democrat ke jagoranta takardun, na tsakanin shekara ta 2015 zuwa 2020.


Wani kakakin Baitun-malin ya ce hukumar ta bi umurnin kotun amma kuma ya ki ya ce uffan game da cewar ko takardun sun kai ga hannun ‘yan kwamitin zuwa yanzu.


Mista Trump ne shugaban Amurka na farko a cikin shekara arba’in da ya yi kememe ya ki bayar da takardun harajinsa.


Ya kafe cewa kwamitin na neman yi masa bita-dakullin siyasa ne kawai.