Home Labaru Birne Mugabe: Shugabanni 20 Za Su Halarci Birnin Harare

Birne Mugabe: Shugabanni 20 Za Su Halarci Birnin Harare

317
0

Shugabannin kasashen Afirka tsaffi da masu ci na ta isa birnin Harare na Zimbabwe domin halartar bikin birne gawar tsohon shugaban kasar marigayi Robert Mugabe.

Cikin su kuwa har da shugaban Equatorial Guinea, wanda ya hau karagar mulki tun kafin Robert Mugabe ya zama shugaban Zimbabwe, fiye da shekaru 40 kenan babu alamar zai sauka daga mukamin.

A halin da ake ciki daga baya dai, iyalan Mugabe, sun hakura sun kuma amince a birne gawar sa a Heroes Acre, wata makabarta ta musamman da ake binne wadanda suka yi gwagwarmaya wajen kwato wa kasar ‘yanci. Da farko dai iyalan gidan marigayin sun so a gina masa wani katafaren daki ne a mahaifar sa, dakin da zai zama makwancin sa na din din din, amma aka yi ta kwan gaba kwan baya har zuwa lokacin da aka shawo kan su.