Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Binciken Gwamnatin Kano Ya Wanke Ado Doguwa Daga Zargin Kisan Kai

Ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, ta ce binciken da ta gudanar
a kan tuhumar da ake yi wa ɗan majalisar wakilai Alhassan
Ado Doguwa bisa laifin kisa ya nuna cewa ba a same shi da
laifin da ake zargin shi ba.

Kwamishinan shari’a na jihar Kano Lawan Musa Abdullahi ya bayyana wa manema labarai cewa, an samu saɓani da dama a cikin bayanan da aka samu daga wajen shaidu.

Ya ce yayin da su ke gudanar da bincike sun gano cewa ma’aikatan asibiti ba su yi cikakken bincike a kan mutanen da ake zargin an harba da bindiga ba, don haka ba a iya tabbatar da cewa an harbe su ba.

Kwamishinan ya kara da cewa, an gudanar da bincike a kan bindigogi da harsasan da ke hannun ‘yan sandan da ke tare da ɗan majalisar a lokacin da rikicin ya faru.

Sai dai a bayanin sa babu wata shaida da ta nuna cewa an yi amfani da bindigogin, kasancewar jami’an ‘yan sandan sun maida daidai adadin harsasan da ke a hannun su.

Exit mobile version