Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bada umarnin a bayyanawa Duniya abinda majalisar tarayya ta kashe a kasafin kudin shekara ta 2018.
Kundin kasafin kudin majalisar da aka fitar mai shafi 45 ya nuna cewa ‘yan majalisar wakilai da kuma majalisar dattawa sun kashe kusan Naira Biliyan 140 daga kasafin kudi na shekarar da ta gabata.
Shugaban majalisar ya ce an warewa majalisa naira billiyan 139 da milliyan dari 5 a cikin kasafin shekara ta 2018, daga cikin kudin naira Biliyan 35 da millyan 5 sun tafi wajen yan majalisar dattawa, sannan kuma naira Biliyan 57 da miliyan 4 sun tafi asusun majalisar wakilai.
Sannan kuma a kasafin kudin shekara ta 2018, an fitar da naira Biliyan 10 da miliyan 2 domin biyan albashin Hadimai da manyan mukarraban ‘yan majalisun tarayyar Najeriya.
Hukumar da ke kula da aikin ‘yan majalisa ta sami fiye da naira Biliyan 2 da miliyan 7, sannan kuma aka fitar da wasu kudi da suka haura naira Biliyan 1 domin wasu aikace-aikacen ‘yan majalisar.