Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Bincike: Daily Trust Ta Ce Sabon Jirgin Saman Najeriya Ya Yi Batar Dabo

Wa su rahotannin daga jaridar Daily Trust sun ce sabon jirgin Nigeria Air’ da tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya gabatar wa jama’a kafin karewar wa’adin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi batar dabo, domin kuwa an neme shi an rasa.

Jaridar Daily Trust ta ce, yanzu haka mutane na ta cece-kuce dangane da inda jirgin ya shiga da kuma lokacin da ake saran ya fara aikin dibar jama’a, tare da neman shafin sa na intanet da zai ba jama’a damar sayen tikiti kai tsaye.

Jaridar tace binciken da ta gudanar ya nuna cewar tuni jirgin ya koma cikin tawagar jiragen ‘Ethiopian Airlines’ inda aka dauko shi domin ci gaba da gudanar da zirga zirgar da ya saba yi.

Wani bincike da jaridar ta Daily Trust ta yi a ranar 1 ga watan Yuni, ya ce an ga jirgin kirar Boeing 737-860 yana zirga zirga tsakanin biranen Addis Ababa da Mogadishu kamar yadda na’urar zirga zirgar jiragen saman da ake amfani da shi ya nuna.

Rahotan binciken ya ce an kwashe kwana 4 ana sauya fasalin jirgin domin mayar da shi cikin jerin jiragen Habasha bayan sauya fentin da aka masa da kuma bikin nuna shi a birnin Abuja.

Jaridar ta ce tayi kokari domin jin ta bakin ma’aikatar sufurin jiragen saman Najeriya dangane da makomar jirgin Nigeria Air, amma shugaban sashen hulda da jama’a na ma’aikatar Odatayo Oluseyi, yaki cewa uffan dangane da lamarin, yayin da majalisar wakilai ta gayyaci babban sakataren ma’aikatar sufurin jiragen sama domin yi mata bayani akan halin da ake ciki.

Exit mobile version