Home Labaru Bincike: Boko Haram Na Amfani Da Jiragen Yaki Marasa Matuki Wajen Kai...

Bincike: Boko Haram Na Amfani Da Jiragen Yaki Marasa Matuki Wajen Kai Hari

944
0

Babbar Jaridar Amurkar nan wanda ta shahara Duniya New York Times, ta bada rahoto cewa sojojin Najeriya sun rasa karsashi wajen yaki da ‘yan ta’ddan Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Rahotannin jaridar sun bayyana cewa akwai cin karo a tsakanin abinda gwamnatin tarayya da jami’ai su ke ikirari na cewa an ga bayan ‘yan ta’dan Boko Haram da ainihin abinda ke faruwa.

Jaridar ta bayyana cewa ‘yan Boko Haram suna aiki ne da manyan na’urori da makamai na zamani ya yin da dakarun Sojojin Najeriya ke amfani da tsofaffin kayan aiki da salo.

Binciken da jaridar New York Times, ta yi a Najeriya, ya nuna cewa sojojin Najeriya suna cikin wani hali na dar-dar da kokarin kare kan su a madadin a ce, sune  ke kai wa ‘yan ta’addan hari a inda suke.

Wasu Sojojin sun shafe shekaru uku suna fagen daga ba tare da sun koma gida ba, saboda haka  makamai da motoci da sauran kayan aikin da ke hannun su, duk sun gaji.

Binciken da jaridar ya kara da cewar abin tada hankalin shi ne yanzu ‘yan ta’ddan suna aiki da jirgin da bai da matuki wanda ake kira ‘Drone.

Fiye da shekaru goma ke nan ana fama da ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya da kuma kewayen Afrika.

Leave a Reply