Home Labaru Bincike : Akwai Yiwuwar A Shiga Kotu Da Elisha Abbo

Bincike : Akwai Yiwuwar A Shiga Kotu Da Elisha Abbo

477
0

Akwai yuyiwar rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gurfanar da dan majalisar  dattawa mai wakiltan Adamawa ta arewa Elisha Abbo a gaban kotu bayan ta kammala bincike.

Rundunar za ta gurfanar Elisha Abbo ne bisa zargin marin wata mata a wani shago a Unguwar Wuse dake Abuja.

‘Yan Sandan sun ce za su dauki wannan matakin ne  bayan an samu faifen bidiyon Sanatan ya na shararawa matar mari.

Idan dai ba a manta ba a ranar juma’a data gabata ne, aka shirya shiga kotu da sabon ‘dan majalisar amma hakan bai yuyiwu ba saboda ba a gama tantance sahihancin faifen bidiyon da a ka samu ba.

Jami’an tsaro su na kokarin tabbatar da ingancin wannan bidiyo ne a matsayin shaida domin gudun kada su gabatarwa Alkali faifen da aka yi wa siddabaru ko kuma kwaskwarima , saboda irin girman wanda ake zargi da laifin.

Leave a Reply