Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Binani Ta Maka INEC A KOTU Kan Soke Ayyana Ta A Matsayin Wadda Ta Lashe Zaben Gwamnan Adamawa

 ‘Yar takarar gwamnan jihar Adamawa ta am’iyyar APC A’isha Dahiru Binani ta sake kai karar hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa.

Binani, wadda lauyan ta Michael Aondoaka ya wakilta, ta gabatar da sabuwar kara a gaban mai shari’a Donatus Okorowo na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

A cikin karar, ‘yar takarar ta bayyana hukumar zabe da jam’iyyar PDP da dan takarar ta Gwamna Ahmadu Fintiri a matsayin wadanda ta ke kara.

A’isha Binani dai ta na neman a binciki hukuncin da hukumar zabe ta yanke na sauya shelar bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaben da Kwamishinan Zabe na jihar Adamawa Hudu Yunusa-Ari ya yi.

Yayin sauraren karar, Aondoaka ya ba da hujjar cewa kotun sauraren kararrakin zabe ke da hurumin tantance makomar wadda ya ke karewa, inda ya ambaci sashe na 149 na dokar zabe ta  shekara ta 2022.

Tuni dai Mai shari’a Okorowo ya dage ci-gaba da sauraren karar bayan ya saurari hujjojin Aondoaka.

Exit mobile version