Home Labaru Bin Sawu: Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Najeriya Nuj Za Ta Fara Yajin...

Bin Sawu: Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Najeriya Nuj Za Ta Fara Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Mai

91
0

Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ ta ce za ta bi sawun ƙungiyar Kwadago ta NLC wajen tsunduma yajin aiki daga ranar Laraba mai zuwa, saboda cire tallafin man fertur.

Ƙungiyar ta NUJ ta bayyana a cikin wata takarda da ta fitar, bayan ganawar da kwamtin gudanarwar ta ya yi domin tattauna batun cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi da kuma matakin ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta ɗauka na shiga yajin aiki a tsakiyar makon da ke tafe ne ita ma ta dauki wannan mataki.

NUJ ta ce a halin da ake ciki tashin farashin man fetur da na sauran kayayyaki sun jefa al’ummar ƙasa cikin mawuyacin hali.

Haka kuma ƙungiyar ta umarci ‘ya’yan ta da ke faɗin jihohin Najeriya su fara yajin aiki tare da fita zanga-zanga daga ranar Laraba 7 ga watan Yuni matuƙar kamfanin mai na ƙasa NNPCL bai janye ƙarin farashin man fetur da ya yi ba.

Leave a Reply