Home Labaru Bikin Ista: Buhari Ya Taya Kiristocin Nijeriya Murnar Bikin Na Bana

Bikin Ista: Buhari Ya Taya Kiristocin Nijeriya Murnar Bikin Na Bana

255
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon taya daukacin al’ummar kirista murnar bukukuwan Ista domin koyi da halaye irin Yesu Almasihu.

Shugaba Buhari ya ce, bikin Ista na da matukar muhimmanci a addinin Kirista, saboda alamun da ke nuna rahamar Ubangiji ga hallitun sa, sannan nasara ce mai haske da ke haskaka duhu.

Mabiya addinin kirista dai na gudanar da bikin Ista ne domin tunawa da ranar gicciye Yesu Almasihu, da kuma nuna soyayya ga juna da kuma kyautata zaman-takewa.

Shugaba Buhari ya taya ‘Kiristocin Nijeriya da duniya baki daya murnar biki tare da fatab za su sa aka a cikin addu’a domin samun nasara a kan al’amuran cigaban kasa.

Leave a Reply