Home Labaru Bikin 12 Ga Yuni: Obasanjo, Jonathan, Gowon, Abdussalam Ba Su Halarta Ba

Bikin 12 Ga Yuni: Obasanjo, Jonathan, Gowon, Abdussalam Ba Su Halarta Ba

341
0

Yayin da bikin ranar Dimokradiyya ya kankama a filin taro na Eagle square da ke Abuja, an nemi dukkan tsofaffin shugabannnin Nijeriya an rasa duk kuwa da an kebe masu mazaunin musamman.

Lamarin dai ya zo da mamaki, kasancewar manyan mutanen a matsyain manyan abokan marigayi MKO Abiola, wanda saboda gwagwarmayar sa aka sauya ranar dimokradiya zuwa 12 ga watan Yuni.

Tsofaffin shugabannin dai sun hada da Janar Yakubu Gowon, da Janar Abdussalami Abubakar, da Janar Ibrahim Babangida, da Olusegun Obasanjo, da Cif Ernest Shonekan.

Alkaluma sun bayyana cewa, Obasanjo ya ki halartar taron ne saboda kunya, domin ya kasance wanda ya ci gajiyar marigayi Abiola, amma har ya gama mulkin sa bai iya yin abin da shugaba Muhammadu Buhari ya yi ba.

Cif Ernest Shonekan kuma an siffanta shi matsayi daya daga cikin wadanda su ka yaudari Abiola, yayin da aka zargi Janar Ibrahim Babangida a matsayin ummul-haba’isin soke zaben da Abiola ya samu nasara.

Leave a Reply