Tsohon Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Malam
Muhammad Garba, ya ce batun Bidiyon Dala ba zai hana
Ganduje samun muƙami ba.
Muhammad Garba ya bayyana haka ne a wani ra’ayin sa da aka wallafa a jaridu, inda ya ke yaba cancantar Ganduje na zama minista ko shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.
Ya ce rahotannin da ake yaɗawa cewa an samu tsaikon naɗa ministoci ne saboda shugaba Tinubu na son janye sunan Ganduje domin naɗa shi shugaban APC na ƙasa, ya karkata alƙamin sa kan waɗanda ya kira ‘yan adawa masu neman ɓata ma shi suna.
Muhammad Garba, ya ce mutanen da ake zargi da ɓata sunan Ganduje, musamman game da dawo da tsohuwar maganar Bidiyon Dala, sun yi haka a shekara ta 2019 domin hana Ganduje zama ɗan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC.
Tsohon kwamishinan, ya ce ya na da yaƙinini cewa matsayin VGanduje a wurin shugaba Tinubu ya kai yadda babu yadda za a yi a hana shi zama ko dai minista ko kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.