Home Labarai Biafra: Za a Iya Warware Matsalar Nnamdi Kanu a Siyasance – Ekwerenmadu

Biafra: Za a Iya Warware Matsalar Nnamdi Kanu a Siyasance – Ekwerenmadu

130
0

Tsohon shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekwerenmadu, ya ce za a iya warware matsalar Nnamdi Kanu a siyasance, sai dai kwararru a fannin siyasa na ganin abin da kamar wuya.

Sanata Ike Ekwerenmadu, ya ce duk da bayanai masu karfi da
shugaba Buhari ya fitar a kan Nnamdi Kanu, har yanzu da shi da
‘yan yankin Kudu Maso Gabas su na ci-gaba da neman hanyar
warware rikicin siyasar da ya shafi Nnamdi Kanu.

Nnamdi Kanu dai ya na fuskantar tuhume-tuhumen da su ka
shafi ta’addanci da kashe-kashen mutane da cin amanar kasa,
lamarin da ya sa ake tsare da shi a hannun jami’an hukumar
tsaro ta farin kaya.

Baya ga kiraye-kirayen da shugabanin Igbo su ka yi yayin da su
ka ziyarci shugaba Buhari, Ekweremadu ya bada misalin irin
tuntubar da ‘yan asalin Igbo su ka yi a lokacin da aka kama
tsohon shugaban MASSOB Ralph Uwazuruike har aka kai ga
sakin shi.

Sai dai wani kwararre a fannin zamantakewar dan Adam kuma
Malami a jami’ar Abuja Dakta Abubakar Umar Kari, ya ce
akwai bambanci tsakanin matsalar Uwazuruike da ta Nnamdi
Kanu.

Leave a Reply