Rikicin kabilanci tsakanin wasu kabilu a jihar Benuwe ya dauki sabon salo bayan wasu ‘yan bindiga sun bude wuta akan wasu mabiya addini kirista a kauyen Tse-Aye da Tse-Ngibo da Ikurav Tiev dake karkashin karamar hukumar Katsina Ala.
An kai harin ne sakamakon gabar dake tsakanin mutanen garin Shitile da na kauyukan Sankera da suka hada da Logo, Ukum da wasu kauyukan karamar hukumar Katsina Ala.
Wani babban jami’in gwamnati da bai yarda a ambaci sunansa ba, ya ce duk kokarin sulhunta mutanen kauyukan ya ci tura saboda a farkon wannan shekarar wasu ‘yan ta’adda daga kauyen Shitile suka kai hari kauyen Ikurav tare da kashe mutane 10.
‘Yan bindigar sun tare musu hanya ne a kauyukan Tse-Ngibo da Tse-Toraye, inda suka kashe mutane 11, wasu kuma da dama suka bazama cikin daji, har yanzu ba a gansu ba.Ya zuwa yanzu dai ba a san takamaiman adadin mutanen da suka kashe ba, domin ba a san inda mutane 40 suke ba.